Sace ma'aikatan jirgin ruwa a gabar Najeriya
July 2, 2020Talla
Kamfanin BW Offshore da ke aikin hakar man fetur, da kuma jigilarsa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis inda ya ce maharan sun kai farmaki ne a kan jirgin ruwan mai suna Senje Berge a kusa da cibiyar mai ta Okwori da misalin karfe hudu da minti 20 wato uku da minti 20 agogon JMT.
Kawo yanzu dai ba a da duriyar ma'aikatan jirgin da aka sace da kuma halin da suke ciki. Sai dai kamfanin na BW Offshore ya ce yana tattaunawa da mahukuntan Najeriya kan batun jirgin wanda ke yi wa kamfanin Addax Petrolium na kasar Chaina aiki a lokacin da 'yan fashin tekun suka fal masa.