1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na karuwa a Maiduguri

December 20, 2018

Sabbin ‘yan gudun hijira na ci gaba da kwararowa zuwa Maiduguri fadar gwamnatin jihar Bornon Najeriya.

Nigeria Flüchtlinge aus Borno
Hoto: DW

Bayan da bayanai suka tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun karbe iko da kananan hukumomin Kukawa da Guzamala da ke arewacin jihar Borno mazauan yankunan sun zabi ficewa daga garuruwan zuwa wurare da suke ganin tudun na tsira ne a Maiduguri, ko kuma wasu yankuna a arewa maso gabashin Najeriya. Tun daga farkon wannan makon daruruwan mutane ke shigowa ta hanyoyin dabam-dabam wasu ta mota wasu kuma suna yanko daji ne inda su ke neman mafaka a Maiduguri. Yawancin ‘yan gudun hijirar mata ne da kananan yara kuma da ganin suna cikin mawuyacin hali. Malam Miuhammad wani ne da ya samu ficewa daga garin Cross Kawwa da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno ya bayyana dalilinsu na ficewa daga garinsu a wannan lokaci da ya ce ya zama dole. Da dama wadannan sabbin ‘yan gudun hijira sun sha bakar wahala kafin su iso nan Maiduguri inda wasu ma sai da aka dauki a Wheel Barrow aka fita da su garin saboda ba za su iya tafiya da kafafunsu ba.
 

Hoto: DW