'Yan sanda sun janye daga bikin 'yanci a Kano
October 1, 2025
Da yawan mutane a Najeriya dai na cewar cikin shekaru 65 da ake bikin an cika bayan samun yancin kai kullum talakan kasar koma baya yake samu lamarin da ya sa tun yana motsawa da samun karkashin kishin kasa har takai a bana ma babu wani bikin murna da aka yi kamar yadda aka saba a kasar lamarin da ke alamta irin fushin da talakawan kasar ke da shi kan salon jagorancin shugabannin kasar.
Ra'ayoyin 'yan Najeriya
Wasu daga matasan Najeriya kenan dake bayyana ra'ayoyin su a wannan rana da ake bikin murnar zagayowar ranar da aka samu yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.
Duk da cewar akwai masu ganin cewar an samu ci-gaba la'akari da wasu alkaluma a kasar amma fa da yawan mutane sun fi hakikancewa da cewar babu wani ci-gaba face na mai hakar rijiya, fatara da talauci tabarbarewar matslar tsaro faduwar darajar ilimi da lafiya su ne muhimman tukwicin da 'yan Najeriya ke cewar suna samu daga shugabanninsu.
Aisha Tamburawa matashiya ce da ke ganin cewar a iya cewar dai ba yabo ba fallasa idan aka duba irin kulli kucciya da ake yi da hankulan talakawan Nigeria.
Matsalolin kasar
To shin me nene matsalar Najeriya ne? tambayar ke nan da yawanci mutane ke yi dangane da yadda aka kasa motsa kasar duk da tarin jama a da arziki da Allah ya albarkaci kasar da shi.
Dr Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne a kwalejin ilimi da share fagen shiga jamia ta Kano, ya ce amsar tana cikin tsarin da ake bi wajen tafiyar da kasar shiyasa ko yaushe yake shan kwaskwarima.
Da yawan matasa dai na cewar wasu lokutan sukan yi tunanin gwara ma da ace Turawan za su sake dawowa su mulke su.
Daga jihar Kano kuwa farraku da zaman cin kunamar kadangare ya kara bayyana a wannan rana da ake wannan biki bayan da kwamishinan yansnadan jihar Kano da tawagarsa suka kauracewa taron na tunawa da samun 'yancin Najeriya shekaru 65 da suka gabata.
Kuma har ma gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya bayyana rashin jin dadinsa tare da Allah wadai da abin da yace cin fuska ne da rundunar ta saba yi masa har ma ya yi kira ga shugaban kasa da ya sauya wa jihar Kano kwamishinan 'yan sanda domin yana ganin wannan ba ya jin maganar gwamnati.lamarin da ke ci gaba da jawo cece-kuce a Kano.