Najeriya: 'Yan sanda sun kama Abba Kyari
February 14, 2022
Talla
An kama kwamishinan sakamakon wata sanarwa da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyin ta bayyana na nemansa ruwan jallo a kan zargin safarar miyagun kwayoyi. A cikin watan Yulin shekara bara ne aka dakatar da kwamishan Abba Kyari daga aiki saboda zargin da aka yi masa na karbar cin hanci daga wani dan Najeriya dan damfara da ke a Amirka Ramos Abbas da aka fi sani da suna Huspuppid da ake tsare da shi a Amirka.