1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Shi'a sun dakatar da zanga-zanga don yin sulhui

Uwais Abubakar Idris MNA
August 1, 2019

Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ta sanar da fara tattaunawar sulhu da gwamnati a kokarin shawo kan zanga-zanga da ta kai ga tashin hankali da rasa rayuka da suke yi bisa tsare shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Nigeria Abuja Proteste von Schiiten des Islamic Movement
Hoto: picture-alliance/AA/A. A. Bashal

Wannan mataki na fara tattaunawa da niyyar sulhu da shi ne irinsa na farko tun daga shekarar 2015 da 'ya'yan kungiyar ta 'yan Shi'a wato IMN suka fara zanga-zanga biyo bayan arangamar da suka yi da sojoji a garin Zaria, ta biyo bayan sanya baki da wasu sarakunan gargajiya na Najeriya da ma tsaffin shugabannin kasar da ba a ambato sunansu ba, wadanda suka lallashi 'ya'yan kungiyar da su maida kube domin zaman lafiya. Muhammad Ibrahim Gamawa shi ne mai magana da yawun kungiyar ya yi karin haske game da gaskiyar wannan lamari.

"Wannan haka ne akwai manya kamar sarakunan gargajiya da tsaffin shugabannin kasar nan da suka nuna rashin jin dadinsu da abubuan da ke gudana, suna kuma tsoron abin da ka iya biyowa baya. Amma gwamnati ta yi ta yin biris, ba ta taba neman ta zauna da mu ba. Sai dai yanzu an zauna da wasu wakilanmu, kuma sun ce za su yi mana bayanin abin da ya gudana."

An sha yin arangama tsakanin 'yan Shi'a da jami'an tsaro a lokutan zanga-zangarsuHoto: Reuters/A. Sotunde

Wannan mataki da mafi yawan al'ummar Najeriya ke murna da bayyana cewa muhimmin ci-gaba ne a kan lamarin da ya kaiwa kowa a wuya, ya biyo bayan garzayawa kotu da 'yan Shi'an suka yi don kalubalantar haramta kungiyar tasu da ma ayyanata a matsayin ta 'yan ta'adda. To sai dai ga Alhassan Dantata Mahmoud na kungiyar tsaro da wanzar da zaman lafiya ya ce babu aibi tattaunawar ko da an ayyanasu a kan hakan.

Kawo yanzu babban mai taimakawa shugaban Najeriya ta fannin yada labaru Mallam Garba Shehu ya ce ba a yi mashi wani karin haske a kan lamarin ba. To sai dai masharhanta a Najeriya irinsu Malam Abdulrahman Abu Hamisu masani a fannin zamnatakewa da siyasar jama'a, na ganin wannan muhimmiyar dama ce da bai kamata a yi wasa da ita ba.

A yayin da 'ya'yan kungiyar ta IMN suka dakatar da duk wata zanga-zanga za a sa ido a ga ko an kama hanyar gano bakin zaren lamarin musamman zaman da kotu za ta yi a mako mai zuwa kan ba da belin shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da shi ne daya daga cikin dalilan wannan tashin-tashina.