1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Aliyu Muhammad Waziri LMJ
November 27, 2025

Al'ummar Najeriya na mika sakon ta'aziyyarsu, dangane da rashin babban malamin addinin Musulunci a darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Najeriya | Bauchi | Ta'aziyya | Sheikh Dahiru Usman Bauchi | Rasuwa
Marigayi Sheikh Dahiru Usman BauchiHoto: Abubakar Sunusi/DW

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sha gwagwarmayar da'awa tsawon shekaru 80, kasancewar ya fara da'awar tun yana da shekaru 20 a duniya karkashin darikar Tijjaniyya. Ya bayar da gagarumar gudummawa wajen yada addinin Musulunci, ba a Najeriya ba kadai har da wasu kasashen Afirka kamar Senegal da Jamhuriyar Nijar.

Bauchi: Jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Usman

02:23

This browser does not support the video element.

Tun bayan sanar da rasuwar shehin malamin, al'umma daga sassa dabam-dabam ke tururuwar shiga jihar Bauchi, domin halartar jana'izarsa. A jihar Kano ana ci gaba da alhinin rayuwar Sheikh Dahiru Bauchin, inda mutane ke bayyana cewa za a jima ana tunawa da gudunmawarsa ga addinin da kuma kyakkyawar mu'amalarsa da mabiya dariku da ma sauran addinai a Najeriyar.

Sheikh Ibrahim Ibn Saleh al-HussainiHoto: Fatima Sheikh Sharif Ibrahim Saleh

Iyalansa sun tabbatar da cewa ya bar wasiyya babban malamin darikar Tijjaniyya Ibrahim Ibn Saleh al-Hussaini da aka fi sani da Shaykh Sharif Saleh ya sallace shi, inda za a binne shi a wani wuri na musamman da aka ware a Masallacinsa da ke cikin garin Bauchi, tun bayan rasuwar babban dansa Dakta Hadi Dahiru Usman Bauchi a 2005.

Tattaunawa da dan Sheikh Dahiru Bauchi

03:15

This browser does not support the video element.

Sheikh Dahiru Bauchi yana daga cikin malaman addinin Musulunci a Najeriya da suka bayar da gudummawa wajen hadin kan al'ummar Musulmi tun kafin samun 'yancin kai, wanda hakan yasa yake da mabiya masu yawa a ciki da wajen kasar. Wasu cikin almajiransa daga wasu kasashe kamar Chadi sun taso sun zauna a wajensa, har kuma zuwa yanzu suka zama tamkar 'yan gida.