1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yunkurin magance matsalar ilimi

Ubale Musa | Salissou Boukari
November 13, 2017

A wani abun da ke zaman sabon yunkurin na kawo karshen rushewar tsarin ilimi aTarrayar Najeriyar masu ruwa da tsaki a harkar ilimin sun yi wani zama domin neman mafita.

Nigeria Studenten in Jos
Daliban Najeriya na tilawaHoto: picture-alliance/epa/Ruth McDowall

Kama daga rashin kwarewa ta malamai, ya zuwa matsalar kayan aiki sannan uwa uba gaza imani a cikin tsarin dai, sannu a hankali harkar ilimi ta na fuskantar tasku a Najeriya. Bayannan kiddidiga na ciki da wajen kasar na neman dora Tarrayar ta Najeriyar kan gaba wajen yawan yaran da basu zuwa makaranta kusan Miliyan 13 a yanzu haka. Wadannan tarin matsaloli ne dai Abujar ke neman sauyawa tahanyar wani taro na masu ruwa da tsaki kan neman shawo kan matsalar ilimin da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar a halin yanzu.

Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan share tsawon lokaci ana tafka muhawara dai ra'ayi ya kusan zama guda game da bukatun da suka kunshi kokari na karin kasafin kudi a fanni ilimin ya zuwa 15 cikin dari na daukacin kasafin kudin kasar anan gaba sannan kuma da ayyana gaggawa a kokari na warware matsalolin da suka yi nasarar rusa imanin kowa a cikin tsarin makarantu na gwamnati. To sai dai kuma ga Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da ya bude taron dai wai irin tsarin da gwamnatin jihar kaduna ta dauka yanzun ne kadai ke iya kai wa ga daidaita matsalar tabarbarewar ilimin da kasar ke fuskanta:

Wasu 'yan makaranta a birnin Lagos na NajeriyaHoto: Reuters/A. Akinleye

"Na saurari ra'ayin wani dan Najeriya da nake girmamawa, ya sheida min cewa bayan ya samu horo anan Najeriya da kuma kasar Amurka da ya koma tsohuwar makarantar Firamaren  da ya kammalla domin ganin irin gudummowar da yake iya bayarwa, cewa ya yi ya kasa gane banbancin da ke tsakanin Malamai da daliban makarantar. Abun da Gwamna El rufa'i ke kokarin yi yanzu shi ne wannan mutumin ya fada min shekaru 10 da suka gabata. Abun takaici ne ace malami ya kasa cin jarabar da ta kamata a yi wa dalibansa don haka muna cikin matsala mummuna."

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani