Najeriya: Kokarin neman dogaro da kai a fannin abinci
August 14, 2019Talla
Wannan mataki dai na cikin jajircewar da Najeriya ta dade tana yi na dogaro da kai a fannin kayan abincin wanda aka zaburar da harkar noma a ‘yan shekarun nan. Tun daga 2015 babban bankin kasar ya haramta samar da kudaden kasashen waje don shigo da kayayyaki har 41 wadanda ya tabbatar za’a iya samar da su a cikin kasar. A yanzu Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya yi mai gaba daya inda ya bai wa bankin umurnin haramta ba da kudadden kasashen waje don shigo da kayan abinci a kasar. Tuni manoma suka fara murna da wannan mataki. Babban bankin Najeriya ya ce daga 2015 zuwa 2018 Najeriyar ta samu adana kudin kasashen waje har dalla bilyan 21 sakamakon haramta shigo da kayan abinci a kasar.