1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta haramta shigo da farantan da ke zuko rana

Uwais Abubakar Idris AH
April 28, 2025

Wata takaddama ta kuno kai a Najeriya bayan da gwamnatin kasar ta dage kan haramta shigo da farantan da ke zuko hasken rana wajen samar da wutan lantarki.

Hoto: Garry Lotulung/Anadolu/picture alliance

Gwamnatin Najeriyar ta bayyana daukan wannan mataki na haramta shigo da farantan da ke zuko hasken rana da ake samar da wutan lantarki saboda sabon yunkurin da take na  fara samar da farantan a cikin  Najeriya.

Inda gwamnatin ta ce tuni ta yi nisa da kafa wadannan masana’antu a Lagos da Enugu da Nasarawa inda  za’a fara samar da farantan da ma batura na Lithium sinadarin da Najeriyar ke da shi sosai.

Dr Abubakar Ibrahim Danbatta kwarrare ne a fanin samar da makmashin da ake sabuntawa ta hasken rana da ke cibiyar samar da makamashi ta Najeriya.

Hoto: Brian Inganga/AP/picture alliance

''Mataki ne da za mu ce mai kyawo domin in aka yi la'akari da cewa zai bunkasa tattalin arziki da samar da ingantaciyyar wutan lantaraki, amma kuma in ka duba za ka cewa masana’antunmu na cikin gida ba su da kwarewar da ake bukata wajen samar da wannan kayan da ake bukata''

Ministan kula da kimiyya da fasaha na Najeriyar   Uche Nnaji ya ce an dai dauki wannan mataki ne a dai dai lokacxin da idanun ‘yan Najeriya ke kara budewa a kan dimbin amfanin da ke tattare da samun wutan lantarki ta hasken rana, domin bayan karin kudin wuta da gwamnatin Najeriyar ta yi hatta masu hannu da shuni na rungumar wannan tsari a yanzu.

Hoto: ACT Government

Kwararru a wannan fanin sun bayyana abin da suke tsoro na cewa gwamnati ta yi sauri na daukan wannan mataki. Mallam Abubakar Atiku daya daga cikin masu harkar samar da wutan lantarki ta amfani da  haskenrana a Najeriyar ya yaba da tsarin.

Hoto: Garry Lotulung/Anadolu/picture alliance

Gwamnatin Najeriyar dai ta bayyana cewa ya zuwa yanzu ta kashe Naira bilyan   200 wajen shigo da irin wadannan faranati daga kasashen waje don haka ya zama wajibi ta dauki mataki a yanzu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani