Najeriya za ta hukunta dillalan haramtattun makamai
July 1, 2021Sama da makamai miliyan 350, ko kuma kaso 70 cikin dari na haramtattun makaman da ke a daukacin yankin yammacin Afirka dai na a Najeriya. Kasar kuma da ta yi nisa cikin kisa da karbar fansa daga ‘yan ina da kisan da ke cin karensu har gashinsa sannan kuma ke barazana ga zaman lafiya a daukacin Najeriyar.
To sai dai kuma daga dukkan alamu mahukuntan kasar na shirin da su farka tare da dauka na matakan rage yawa na makaman da mafi yawan su ke fitowa daga Libiya. Kuma na baya-baya cikinsu dai na zaman wata sabuwar doka da majalisar dattawar kasar ta kaddamar, da kuma a cikin ta dillallan na makamai na haramun ke shirin fuskantar dauri na shekaru uku a gidan yari, ko bayan tarar da ta kai Naira miliyan uku.
Sabuwar dokar dai da ke zaman gyaran fuska bisa tsohuwar da ta tanadi tarar Naira dubu daya dai na zaman sabon fata ga Abujar da ke neman hanyar kai karshe na kwarara ta makaman babu ka'ida.
To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba dai dokar ta fara fuskantar adawa daga sassa daban-daban da ke mata kallon ta kasa. Har a cikin majalisar dai alal misali, ana kallon sabuwar dokar ta yi kadan ga kokarin tunkarar matsalar da ke zaman daya cikin kalubalen tsaro mafi girmq cikin kasar a halin yanzu.
Arewacin Najeriyar dai na zama na kan gaba cikin matsalar ta bazuwar makaman da ko dai ke cikin ayyuka na ta'addan kudu maso gabashin kasar ko kuma satar shanun da ta addabi arewa maso yamma da ma tsakiyar cikinta. Kuma ko a tsakanin masana dai ana kallon gazawar dokar da ta manta da irin zakin da ke akwai cikin sabon cinikin na makamai a kasar ba.
Captain Abdullahi Bakoji dai na sharhi bisa harkar ta tsaro, da kuma ya ce gatan ‘yan laifin a tsakanin al'umma ya sa da kamar wuya dokar ta yi tasiri ba tare da barazana ga rayuwar dillallan makaman ba.
To sai dai kuma in har daurin na shekaru uku ba ya tasiri a kokarin rage makamai a gari, ga Yahuza Getso, siyasa ta kasar da ta tanadi makamai har ga masu taka rawa a cikinta dai, ko bayan hanci na jami'an tsaron da ke yakar bazuwa ta makaman ya sa ba bambanci a tsakanin dokar da tatsuniyar cikin dare a dakin kaka. Rage tasirin makaman dai na zaman gada tsakanin Najeriyar da kaiwa ya zuwa zaben da ke iya burge ‘yan kasar da ma bakinta.
Tuni dai hukumar zabe ta kasar ta ce zaben na shekara ta 2023 na fuskantar barazana sakamakon tashin hankalin da makaman ke rurawa.