Najeriya za ta kara kudi a fannin tsaro
December 14, 2017Talla
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya shaida wa manema labarai a Abuja babban birnin kasar cewar, yabawar da gwamnonin kasar suka yi da irin cigaban da aka samu a bangaren yaki da Ta'addanci, shi ne dalilinsu na amincewa da a fidda dala biliyan daya daga asusun don cigaba da yakar ayyukan ta'addanci a kasar.
An dai tsayar da lokacin sabon zaben shugaban kasa da gwamnaonin Najeriya a watan Fabarairu zuwa watan Maris na shekara ta 2019,lamarin da tarihin ya nuna shike zaburar da 'yan siyasa wajen satar kudaden kasar.