Ja'maa na ci gaba da fitowa
February 23, 2019![A nan wata mazabar ce a Jihar Zamfara inda jama'a ke jefa kuri'a](https://static.dw.com/image/47655736_800.webp)
Talla
'Yan bindiga sun kai hari a Maiduguri da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya sa'o'i kalilan kafin bude runfunan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, lamarin da ya tilasta wa mutane gudu gabanin fara kada kuri'a. To sai dai a halin yanzu al'amura sun daidaita kuma jama'a na ci gaba da halartar runfunan zabe domin ka'da kuri'unsu.