Najeriya: Zaben cike gurbi a jihohin Bauchi da Katsina
August 10, 2018Yanzu haka hankali jama’a a jihar Bauchi musamman a mazabar Bauchi ta Kudu kan zaben cike gurbi ne da za a gudanar na kujerar Sanata mai wakiltar wannan mazaba a majalisar dattawa ta kasa, lamarin da ke zuwa bayan wata biyar da rasuwar Malam Ali Wakili wanda kafin rasuwarsa shi ne ke kan kujerar.
Wannan zabe dai na zuwa ne a dai dai lokacin da jam’iyya mai mulki a kasa ke cikin matukar bukatar karin magoya baya a majalisar Tarayya domin samun rinjaye da zai bai wa gwamnatin kasa damar aiwatar da ayyuka yadda suka kamata.
Batun ‘Sak’ wato zaban kowane dan takara da jam’iyya mai mulki ta tsayar, yana daga cikin abin da jam’iyyar ta PDP ke kira ga jama’a da su kauce wa sake fadawa cikinsa, domin a cewar shugaban kwamitin yada labarai na jihar Bauchi Alhaji Garba Doya ai yanzu kan jama’a ya waye don haka ne suke da kwarin guiwar samun nasara a wannan zabe.
A jihar Katsina ma dai haka batun yake inda can ma ake zaben cike gurbi na dan majalissar dattawa na shiyar Daura. Zaben dai na matukar daukar hankalin ‘yan kasa kasancewarsa zabe ne na mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wani gangami na jami'iyyar APC kan zaben, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sha alwashin ganin sun lashe zaben don fidda shugaban kasa daga kunya, musamman ganin yana fuskantar kalubale da ficewar da wasu a majalisar dattawan kasar suka yi a baya-bayan nan.