1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude runfunan zabe a Najeriya

February 25, 2023

A wannan Asabar al'ummar Najeriya kasa mafi yawan al'aumma a nahiyar Afirka ke kada kuri'ar zaben shugaban kasa da 'yan majalisun wakilai da kuma dattawa na kasar.

Najeriya I Zaben shekara ta 2023
Zaben NajeriyaHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Zaben na wannan shekara na gudana ne cikin yanayi na dagulewar al'amuran tsaro da kuma matsin tattalin arziki sakamakon canja tarkadun kudin kasar.

Sama da masu zabe miliyan 87 ne za su zabi daya daga cikin 'yan takara 18 dake zawarcin kujerar shugaban kasar a mazabu dubu 176 da aka tanada a sassa daban-daban na kasar.

Masu zaben NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Sai dai rahotanni na cewa sama da mutane miliyan shida ba za su samu zarafin yin zaben ba sabili da rashin karbar katin zabensu yayin da a wasu sassan kasar hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa ba za a bude runfunan zaben ba saboda dalilai na tsaro.

An buda runfunana zaben ne da karfe bakoye da minituna 30 agogan kasar sai dai masu aiko da rohotanni sun akwai yuwuwar matsalar tsaro ta kawo cikas ga zaben wanda za a sanar da sakamakon sa kwanaki 14 bayan kidayar kuri'un da 'yan kasar suka jefa.

Zaben Najeriya na wannan shekara ta 2023 dai da duniya ta zuba ido wanda kuma aka tanadi na'urorin zamani domin gudanar da shi na da matukar mahinmanci ga 'yan kasar da suke sa ran samun sabon shugaban da zai dawo da martabar Najeriyar a fannin tattalin arziki da kuma tsaro.