1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zanga-zanga a matsayin makami

Mouhamadou Awal Balarabe
July 28, 2022

A yunkurin matsin lamba ga gwamnatin tarayya don kawo karshen yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU, 'yan kungiyar kodago NLC sun bi sahun malamai wajen gudanar da gangami da zanga-zangar gargadi a sassa Najeriya

Nigeria Protest NLC Abuja
Hoto: Uwais/DW

Kungiyar kodago ta NLC ta ce ta yanke shawarar tsunduma hannu da kafa cikin zanga-zangar gargadi ne bayan kallo daga nesa na tsawon watanni biyar daga nesa ba tare da nuna alamun shawo kan rikicin malaman jami'o'in Najeriya da ke barazana ga karatu a kasar ba. Naira Triliyan guda da doriya ne malamanjami'o'in ke bukata don ci gaba da raya harkar ilimin da ke lalacewa, lamarin da ke haddasa hijirar 'ya'yan manya zuwa kasashen waje.

Dalar Amirka miliyan 357 ne dai babban banki na kasar ya ce mahukuntan kasar sun bayar cikin watanni uku da suka gabata da nufin tura 'yan kasar zuwa kasashen wajen neman samar da karatu mai kwari bayan rushewar lamura a jami'o'in kasar.

Zanga zangar dai na zaman matakin farko a  jerin matakai na masu kodagon da nufin matsa lambar mahukunta don su kawo karshen yajin aiki. Sai dai kungiyar malaman ta  ASUU ta ce tana shirin tafiya yajin aiki in har masu mulkin na Abuja suka kasa shawo kan matsalar 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna