Najeriya: Zargin gwamnati da dakile adawa
December 15, 2025
Tuni dai fadar gwamnatin Najeriyar ta musanta wannan zargi, inda ta ce babu gaskiya a cikinsa. Ya zuwa yanzu kimanin ministocin tsohuwar gwamnatin marigayi tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari biyu ne ke hannu na jami'an Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta kasar EFCC, ko bayan wasu kusan biyar da hukumar ke bincike a kan zargi na laifuka dabam-dabam.
Ana kuma kallon tururuwar komawar gwamnonin adawa zuwa cikin gidan APC, a wani abun da ya tayar da hankalin masu adawar Najeriyar a halin yanzu. Wata sanarwa ta gamin gambiza da 'yan adawar kasar suka fitar, ta yi nunin yatsa ga Shugaba Tinubu tare da zarginsa da neman hadiye adawar kan hanyar tabbatar da ikonsa.
Najeriyar dai a fada ta sanarwar na kallon wani yunkurin neman kwace iko na siyasa a kasar, ta musgunawa masu adawar maimakon zuwa rumfar zabe a cikin neman kuri'a. Koma ya zuwa ina adawar ke shirin ta kai da nufin aiken sako bisa rawar EFCC a kokarin danne su dai, fadar gwamnatin kasar ta ce babu gaskiya cikin zargin banbanta tsakanin yan APC da masu adawar a cikin yakin hancin.
Kokari na danne adawa ko kuma laifi tudu ka hau ka hango na wani, zargin na adawa dai na kara fitowa fili da irin sabon nau'in siyasar da ake a Najeriyar a halin yanzu. Sannu a hankali dai, kasar tana dada nisa a cikin tsarin ko mutuwa ko yin rai cikin batu na neman karbar iko a zabukan da ke tafe.
Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin siyasa ta kasar, kuma ya ce kazanta ta mamaye cikin gidan 'yan mulkin da ma na adawar tun tsawon lokaci. Kokari na kare doka ko kuma wayon a ci dai, sannu a hankali fagen siyasar Najeriyar na neman komawa gwagwarmaya ta mamaye arzikin kasa tsakanin beran birni da na kauye.