1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira a kan hukunta barayin 'yan Chibok

Uwais Abubakar Idris LMJ
August 19, 2021

Bayan mika wuya da wasu cikin wadanda suka sace 'yan mata 'yan makarantar sakandaren garin Chibok a Najeriya suka yi, wasu kungiyoyi na kira da a tabbatar an hukunta 'yan bindigar da suka yi sace su.

Nigeria 21 Chibok-Mädchen
Shekaru biyu bayan sace 'yan matan Chibok, wasu cikinsu sun kubutaHoto: Picture-Alliance/Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP

Shekaru bakwai kenan da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da 'yan matan daga makarantarsu da ke garin Chibok a jihar Borno. Kubutar biyu daga cikinsu dai, ta haifara da sabon fata bayan daukan dogon lokaci na fitar da rai a kan al'amarin nasu. 'Ya'yan kungiyar mayakanBoko Haram din dai, sun mika wuya tare da 'yan mata biyu wato Ruth da Hassana cikin wadanda suka yi garkuwa da su. Matakin mayakan dai, ya sanya kungiyoyi na yin kira da a hukunta wadanda suka sace su tare da yi musu auren dole, abin da Hosea Tsambido Abana na kungiyar BBOG ya ce kuskure ne ma a ce aurensu suka yi.

Najeriya: Leah Sharibu a hannun B.Haram

02:37

This browser does not support the video element.

Ita ma kungiyar CSWN da ke nuna kawance, ta bukaci a tabbatar da nemawa 'yan matan adalci ta hanyar hukunta wadanda suka sace tare da yi wa 'yan matan auren dole, kamar yadda shugaban kungiyar Reuben Buhari ya bayyana cikin wata sanarwa. Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun 'yan bindigar na mika kansu ga sojojin Najeriya. A yayin da Najeriyar ke murna da wannan nasara ta mika kai da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi, masharhanta na ganin babban aiki a gaba shi ne na yafiya da karbarsu su zauna cikin al'umma domin wanzuwar zaman lafiya. Yafiya dai, na zaman muhimmin ginshiki a dukkanin manyan adinan Najeriyar biyu.