1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari: Najeriya ta samu ci gaba a cikin shekaru 20

June 12, 2019

Ana gudanar da bikin ne na ranar ta dimukaradiyya 12 ga watan Yuni a maimakon 29 ga watan Mayu, kuma a cikin jawabin da ya yi shugaba Muhammadu Buhari ya ce an samu ci gaba a Najeriyar a cikin shekaru 20.

Nigeria Democracy Day 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Bikin na ranar dimukaradiyya ya gudana a gaban shugabanni na kasashe sama da 20 wanda suka halarci bikin, tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da babban filin wasa na kasa da ke a Abuja a matsayin filin kwallon MKO Abiola. Ranar ta zo ga  shi kansa shugaban kasar da ke jawabinsa na farko ga 'yan kasar bayan sake dare mulki zuwa mataki na  gaba. Cikin wani dogon jawabin da ya dauki sama da mintuna 30 dai shugaban ya ce gwamnatinsa za ta dora a biasa ci gaban da ta samu shekaru Hudu baya. Wannan biki dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun hare-hare a Najeriya na kungiyar Boko Haram wanda Buhari ya ce gwamnatinsa na faman kawo karshen 'yan ta'addar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani