Najeriya: Masu garkuwa da mutane sun addabi jama'a
April 4, 2019Talla
Wannan al'amari dai da farko an dan samu saukinsa amma kuma daga baya-baya nan lamarin ya kara lallacewa. A kasa da mako dai kawai sama da mutane guda 30 aka sace tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Hanyar jirgin kasa ta fi tabbas fiye da ta mota saboda masu yin sata da yin garkuwa jama'a
Darurruwan jama'ar ne a Jihar Kauna ta Najeriya ke yin tururruwar zuwa daukar jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja domin kaucewa masu yin fashi a kan hanyoyin mota. Wadanda ke satar mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudaden fansa. Duk da irin kokarin da 'yan sanda suke yi na ciwo kan al'amarin har yanzu da sauran rina a kaba.