1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar rashin abinci da tsaro a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 10, 2024

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa a kan yawan alummar Najeriya da ke fuskantara karancin abinci, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin kasar.

Najeriya | Shirin Samar da Abinci | Majalisar Dinkin Duniya | Karancin Abinci | Tsaro
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi gargadi kan yunwa a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar ya nunar da cewa, sama da 'yan Najeriya milyan 26 ne ke fuskantara barazanar yunwa baya ga barazanar rashin tsaro da ke shafar aikin gona. Wannan matsala ta rashin wadataccen abinci da ta haifar da barazanar da yunwa ke yi wa alumma a Najeriyar na ci gaba da daga hankalin Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar ne, a daidai lokacin da yake kukan rashin wadataccen kudin samar da abinci ga mutanen da suka rasa mahalansu a yankin Arewa maso Gabashin kasar. Daraktan shirin a Najeriya David Stevenson ya bayyana halin da ake ciki na rashin tsoro, a matsayin abin da ke kara yin illa musamman kai hare-hare a daidai lokacin da damina ke kankama.

Sakkwato: Cinikin kayan abinci

03:19

This browser does not support the video element.

Ana danganta tsadara kayan abinci da barazanar da yunwa ke yi wa sama da mutane milyan 26 a Najeriyar da batu na rashin tsaro da ke addabara kasar musamman a yankinn Arewa maso Yamma da ake noma mai dimbin yawa, inda hare-haren 'yan bindigar daji suka hana noma da kiwo. To sai dai a Arewa maso Gabashi bullowar karin sababbin hare-hare na kunar bakin wake, na daga hankalin Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar. Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta bayyana daukar matakai, inda ta bayar da iznin shigo da kayan abinci daga ketare ba tare da haraji ba har tsawon wani lokaci. Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne, domin ceto al'ummar kasar daga barazanar da suke fuskanta ta shiga matsalar yunwa sakamakon tsadar rayuwa musamman ma kayan abinci.