1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nakiya ta hallaka mutum 10 a Najeriya

April 18, 2024

Mutum goma sun rasu, 23 kuma sun jikkata yayin da wata motar da ke dauke da 'yan kasuwa ta taka nakiya a arewa maso gabashin Najeriya.

Sojan Najeriya a shingen bincike
Sojan Najeriya a shingen bincike Hoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

Lamarin ya faru ne ranar Laraba yayin da wani ayarin manoma da masunta suka taso daga garin Monguno a kan hanyarsa ta zuwa Tafkin Chadi.

Motar ta a kori kura ta taka nakiyar ce da ake zaton 'yan kungiyar ISWAP ne suka dasa ta kamar yadda majiyoyin suka  bayyana.

An fatattaki masu tada kayar baya a yankunan da suka kwace shekarun baya a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

 Amma har yanzu suna kai hare-haren kwanton bauna tare da far wa motoci da ke tafiye-tafiye a wajen gari.