Namibiya: 'Yan kasar sun bukaci biyan diyya
May 29, 2021Hukumomi a Namibiya sun bayyana farin cikinsu dangane da abin da gwamnatin Jamus ta yi na amince wa da kuskuren da ta yi na kisan kare dangi a kan kabilun Herero da Nama a zamanin mulkin mallaka.
Jamus dai ta yi mulkin mallaka a yankin da yanzu ya kunshi kasar Namibiya, inda Jamus din ta bayyana kudurinta na bayar da gudunmawar Euro biliyan daya da miliyan dari uku don ayyukan raya kasa a Namibiya a maimakon diyya.
Sai dai wasu 'yan Namibia mazauna Jamus sun bukaci gwamnatin ta Jamus ta biya diyya ga iyalan mutanen da aka hallaka a zamanin mulkin mallaka maimakon gudunmawar raya kasa da za ta bayar.
Batun tallafin dai ya zo ne sakamakon wata zanga-zanga da ta barke a kasashen biyu na Jamus da Namibiyar kan bukatar biyan diyyar wadanda Jamus din ta hallaka da kuma daukar nauyin wasu manyan ayyukan cigaba a kasar da aka yi wa mulkin mallaka a maimakon ban hakuri kawai.