1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Narendra Modi ya tsallake rijiya da baya

Abdoulaye Mamane Amadou
June 4, 2024

Kawancen jam'iyyun da ke mulki a Indiya na kan hanyar lashe zaben da aka gudanar duk da koma bayan da suka na kasa samun rinjayen da suke bukata a majalisar dokoki.

Firamnistan Indiya Narendra Modi
Firamnistan Indiya Narendra ModiHoto: Punit Paranjpe/AFP/Getty Images

Sakamakon da aka fitar a yanzu na nuni da cewar jam'iyyar BJP ta firaminista Narendra Modi ta samu gagarumin koma baya, domin kuwa ba za ta samu gagarumin rinjayen da take bukata ba a majalisar dokoki wanda masana ke cewa da alama hakan ka iya kawo mata tangarda wajen tabbatar da manufofinta na kafa cikakkiyar gwamnati.

Karin bayani :  Manoma a Indiya sun bukaci karin farashi

Sakamakon na nuni da cewa jam'iyyar 'yan hamayyar Indiya ta kara ninka kujerunta a zaben inda ake hasashen adadinsu na ninka har sau biyu bayan da ta samu ruwan kuri'u a sassa da dama na kasar Indiya.

Karin bayani :  Jam'iyyar BJP a Indiya na son jan hankalin Musulmi a Kashmir

Firaminista Modi mai shekaru 73 da aka sake zaba a mazabar sa ta Varanasi, ya bayyana cewa al'ummar Indiya sun kada wa jam'iyyarsa kuri'a da gagarumin rinjaye, sun kuma nuna na'am da sauye-sauyen da ya aiwatar.