Ana ci gaba da gwabza fada a garin Sirte
June 22, 2016Talla
Kungiyar IS dai na neman mamaye kasar Libiya. Rahotanni sun nunar da cewa dakarun sun samu nasarar kwace iko da wata babbar hanya da kuma gidan radiyo na garin na Sirte a wani gagarumin bata kashi da suka yi da mayakan kungiyar ta IS. Ko da yake rundunar sojojin na Libiya ta yi asarar a kalla sojoji 84 tun bayan fara gwabza fada tsakaninsu da mayakan na IS a ranar Talatar da ta gabata yayin da wasu 135 suka jikkata, sun samu gagarumar nasara a wannan arangama. Rundunar sojojin ta Libiya dai ta sanar da cewa tun bayan da suka fara fafatawa da 'yan IS din cikin watan da ya gabata kawo yanzu, sojoji 220 ne suka halaka.