Zaben Donald Trump ya haifar da mahawara
November 10, 2016![US-Präsidentschaftswahl 2016 - Sieg & Rede Donald Trump](https://static.dw.com/image/36319348_800.webp)
Talla
Duk da cewar binciken jin ra'ayin jama'a da ma sauran masu lura da al'amuran siyasa sun bai wa 'yar takara Hillary Clinton nasara kafin zabe, amma 'yan kasar Amirka sun tabbatar da dan takara Donald Trump a matsayin sabon shugaban kasar Amirka wanda zai maye gurbin Shugaba Barack Obama.