1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarori da ake samu a kan cutar HIV a Najeriya

Maawiyya Abubakar Sadiq M. Ahiwa
December 1, 2022

A kowace ranar daya ga watan Disamba, duniya na nazarin nasarorin da aka samu wajen yaki da cutar HIV/AIDS. A bana, mahukunta a Najeriya sun ce ana samun nasara.

Magungunan rage kaifin kwayar cutar HIV
Magungunan rage kaifin kwayar cutar HIVHoto: BARBARA DEBOUT/AFP/Getty Images

Yayin da daya ga watan Disamba ke ranar masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV a fadin duniya, gwamnatin jihar Sokoto a Najeriya ta ce tana samun nasara wajen takaita bazuwar cutar, tare da shan alwashin dakile ta a fadin jihar.

A jihar Sokoto alkalumman masu dauke da wannan cuta mai karya garkuwar jiki sun haura sama da dubu 12, to amma hukumomin jihar sun bayyana irin fadi tashin da suka rika yi da ya samarda nasarar da suka samu ta zakulowa tare da dora mutane masu dauke da wannan cuta su sama da dubu 11 a kan magungunan da ke rage kaifi da kuma radadin cutar.

Baya ga aikin hadakar yin gangamin wayar da kai da sauran hukumomin da ke yaki da wannnan cuta mai karya garkuwar jiki, yanzu haka dakunan karbar magunguna rage kaifi da kuma radadin cutar 14 ne hukumomin jihar ta Sokoto suka samar.

Hoto: Heiner Heine/imageBROKER/picture alliance

A shekarun 1988 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar daya ga watan Disamba a matsayin ranar masu dauke da wannan cuta domin wayar da kai da kuma nuna kauna ga masu cutar , bugu da kari da jimamin wadanda suka rasa ‘yan uwansa kan cutar, da ma bitar halin da ake ciki.

Ko da a shekarar 2014, sai da gwamnatin jihar Sokoto ta samar da wata dokar ba da kariya ga masu cutar, kuma taken ranar a bana shi ne samar da daidaito don yaki da wannan cuta ta HIV nan da shekara ta 2030, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ke muradi.