1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kare kanta game da makamai masu Linzami

Zulaiha Abubakar MNA
November 1, 2018

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bukaci Rasha ta yi bayani game da sabbin makamai masu linzamin da ta mallaka lamarin da ya ci karo da sharuddan da kungiyar ta tsara.

NATO Jens Stoltenberg Brüssel
Hoto: Reuters/F.Lenoir

Wannan kira na zuwa ne yayin ganawar jakadun kungiyar tsaro ta NATO da takwaransu na kasar Rasha a ranar Laraba bayan babban sakataren kungiyar tsaron ya bayyana yadda kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Rasha ta karya dokar da ta haramta mallakar nau'in wasu makamai masu linzami tsakanin kasashen kawance, lamarin da ya ce na zaman barazana ga wasu kasashen Tarayyar Turai.

A nata bangaren Rasha ta baiyana cewar ko kadan mallakar wadannan sabbin makamai masu linzami bai ci karo da dokar da kungiyar tsaron ta yi tanadi tun a shekara ta 1987 ba.