NATO ba za ta shiga yakin Ukraine ba
March 17, 2022Talla
Ganawar ta su na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelenskyy ya yi jawabi gaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta kafar bidiyo.
A jawabinsa shugaba Scholz ya yaba da kalaman shugaba Zelenskyy, sai dai kuma ya na mai jaddada dalilin da ya sanya kungiyar tsaron NATO ta gaza shiga tsakani da karfin soji. Scholz ya kara da cewa shigar kungiyar cikin yakin ka iya kara rura wutar rikicin da ba a san idan zai tsaya ba. A nashi bangaren, Stoltenberg ya ce aikin kungiyar shi ne kwantar da tarzoma.
Ukraine dai ta sha yin kira ga kungiyar NATO da ma kasashen Turai da su kai mata dauki mussaman a babban birnin kasar Kyiv.