NATO da EU sun hadin gwiwa don yaki da matsalar bakin haure
November 28, 2021Kungiyar Tarayyar Turai da takwararta ta tsaro NATO sun jaddada matsayarsu na hada karfi da karfe dan tunkarar matsalolin bakin haure da 'yan gudun hijira a iyakar Belarus da Poland da kuma barazanar da suka ce Rasha ke yi a iyakarta da Ukrain. A yayin wata ziyarar aiki ta hadin gwiwa a Lituweniya sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg da shugabar kungiyar EU Ursula von der Leyen, sun zargi Belarus da yunkurin hadasa matsalar bakin haure da gangan a wani mataki na dagula al'amura. Shugabar kungiyar EU Ursula von der Leyen ta ce "Za mu kara linka kudaden da muke samarwa wajen tabbatar da tsaro iyakokin kasashen nan musamman Lituweniya da ke da iyaka mai tsawo." Ziyarar hukumomin biyu dai na zuwa ne a yayin da ake jajibirin taron koli na ministocin harkokin wajen NATO a wannan Talatar, wanda kuma ake sa ran babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken zai halarta.