Kungiyar tsaro ta NATO za ta yi taro kan Rasha
September 6, 2020Talla
A nata bangare ita ma kungiyar tarayyar Turai ta ce akwai yiwuwar ta dauki wasu kwararan matakan ladabtarwa ga kasar Rasha, inda babban jami'in huldar diflomasiyarta Josep Borrell, ya bukaci hukumomin Moscow da su bayar da hadin kai tare da kaddamar da cikakken bincike.
A ranar 22 ga watan jiya ne aka kwantar da madugun 'yan adawar ta Rasha Alexeï Navalny a wani asibintin soja da ke Berlin na nan Jamus, kana daga bisani wani binciken kwararru ya tabbatar da cewa ya shaki guba ce mai sarke jijiyoyi da ake kira Novitchok.