1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: NATO da EU sun lashi takobin kakkabe Rasha

January 10, 2023

Duk da hadin kan da NATO da EU ke da shi sun ce a yanzu sun kara kulla alakar fatattakar Rasha daga Ukraine bayan wata yarjejeniya da suka rattaba hannu a kanta.

Hoto: Olivier Matthys/AP Photo/picture alliance

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da Kungiyar Tsaro ta NATO sun rattaba hannu a kan wata sabuwar yarjejeniyar karfafa aiki na bai-daya domin dakatar da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine da ma samar da wadaccen tsaro a nahiyar Turai.

Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta EU Ursula von der Leyen da shugaban Majalisar Turai Charles Michel da sakatare janar na NATO Jens Stoltenberg ne suka rattaba hannu a kan wannan yarjejejeniya a Talatar nan a kasar Beljiyum, inda sakatare janar na NATO ya ce bangarorin biyu sun bude sabon babi.

Shugaban na kungiyar tsaro ta NATO ya kuma an karar da kasashen Turai cewa burin shugaban Rasha shi ne cutar da nahiyar Turai, yana mai gargadin su da cewa ya kamata su shirya tunkarar wannan kalubale.