Atasayin sojin NATO a Norway
March 14, 2022![Ukraine | Internationale Manöver „Rapid trident“ im Jahr 2019 in Yavoriw](https://static.dw.com/image/59541379_800.webp)
Talla
Atisayin wanda aka dade da tsarashi, na da manufar auna karfin kasar ta Norway na samun ƙarfafawa daga waje a yayin da wata ƙasa ta kaimata hari. Jiragen yaki sama da 200 da na ruwa kusan 50, ke cikin atisayin da za a kai har daya ga watan Afrilu ana yin sa, sai dai wani kakakin rundunar sojin Norway ya ce atisayen ba ya da alaka da yakin Ukraine. Kudirin da ke a ƙarƙashin sashe na biyar na yarjejeniyar NATO shi ya wajabta mambobinta su ba da taimako ga ɗa yansu da ke fuskantar barazana.