1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO: Nazari kan tsaron tekun Baltic

Abdullahi Tanko Bala
January 14, 2025

Kasashe mambobin NATO da ke yankin tekun Baltic na taro a Helsinki domin nazarin dabarun kare kare bututun makamashin gas da wayoyin sadarwa a karkashin teku.

Jirgin ruwan Rasha a tekun Baltic
Jirgin ruwan Rasha a tekun BalticHoto: Vitaly Nevar/TASS/dpa/picture alliance

Shugabannin kungiyar kawancen tsaro ta NATO sun hallara a birnin Helsinki na kasar Finland domin tattauna kalubalen da ake fuskanta a tekun Baltic

Hakan dai na da nasaba da abin da ya faru na lalata wasu manyan turakun makamashi gas da wayoyin sadarwa a karkashin teku a farkon lokacin da Rasha ta kai wa Ukraine mamaya a 2022.

Shugaban kasar Latvia Edgar Rinkevics ya ce a yanayin da jiragen ruwa fiye da 2000 suke ratsawa ta tekun a kowace rana, zai matukar wuya a iya kare dukkan wayoyin na karkashin teku.

A waje guda kuma a yayin da shugabannin ke hallara, gidan talabijin din Poland ya ruwaito wani sabon lamari na jirgin ruwan Rasha, yana shawagi a tekun na Baltic kusa da bututun gas da ya taso daga Norway zuwa Poland.

Shugabannin Denmark da Eastonia da Finland da Jamus da Lativia da Lithuania da Poland da kuma Sweden tare da kwamshinar kula da fasaha da tsaro ta tarayyar Turai Henna Virkkunen da kuma sakataren kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte ke halartar taron.