Rasha na gab da karbe iko da garin Bakhmut
March 8, 2023Talla
A bayaninsa ga manema labaru a birnin Stockholm na kasar Sweden a gefen taron ministocin tsaron kasashen EU, Jens Stolternberg ya ce dakarun na Moscow sun sami mumunan koma baya a kokarin kwace wannan gari, amma kuma ba za a boye gaskiyar da ke nuna cewar wannan gari na gab da fadawa hannunsu.
Stoltenberg ya ce akwai bukatar ci gaba da tallafa wa sojoin na Kyiv, bayan wani ikirari na kamfanin Wagner da ke cewar sun yi nasarar mamaye gabashin birninn na Bakhmut da ke da manyan masana'antu.
Gumurzun karbe iko da wannan gari dai na zama mafi tsawo a tarihin mamayar da rasha ta kwashe shekara ta na yi a kasar ta Ukraine.