1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

NATO: Scholz ya yi maraba da girke makamai a Jamus

July 11, 2024

Shugaban na gwamnatin Jamus ya nuna farin ciki kan matakin na Amirka inda ya ce abu ne da zai samar da zaman lafiya.

Shugaban Amirka Joe Biden tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a taron NATO na 2024
Shugaban Amirka Joe Biden tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a taron NATO na 2024Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya yaba wa matakin da Amirka ta dauka na girke makamai masu linzami da ke cin dogon zango a kasarsa domin nuna turjiya.

Olaf Scholz ya fada wa manema labarai a taron NATO da ake rufewa ranar Alhamis cewa abu ne na tabbatar da zaman lafiya da nuna turjiya sannan mataki ne mai muhimmanci a lokaci mafi dacewa.

Sabon firaminista ya yi alkawarin sake gina kasar

A ranar Laraba ce Amurka ta sanar da matakin karfafa NATO a Tarayyar Turai akan Rasha, ta hanyar fara girke manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zango a Jamus daga 2026.

A martanin da ta yi kan matakin a wannan Alhamis, Rasha ta ce ta na shirin daukar matakin da ya dace domin dakile barazanar NATO.

Taron NATO na kwanaki uku yana gudana ne a kasar Amirka daidai lokacin da kungiyar tsaron ke cika shekaru 75 da kafuwa, inda yanzu take da mambobi 32, kuma take zama kawancen tsaro mafi girma da tasiri a duniya.