1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO ta kakkabo jiragen yakin Rasha a samaniyar Estonia

September 20, 2025

Estonia ta bukaci kungiyar tsaro ta NATO ta gudanar da taron gaggawa bayan da jiragen yakin Rasha suka keta sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba. Sai dai Moscow ta musanta lamarin.

Jiragen yakin Rasha sumfurin MiG-31
Jiragen yakin Rasha sumfurin MiG-31 Hoto: Alexander Strela/Zoonar/picture alliance

Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da cewa ta kakkabo wasu jiragen yakin Rasha guda uku sumfurin MiG-31 da suka kutsa sararin samaniyar kasar Estonia ba tare da izini ba, lamarin  da kasashen Turai suka bayyana a matsayin ganganci.

Firaministan Estonia Kristen Michal, ya ce kasarsa ba za ta laminci wannan lamari ba, sannan ya bukaci NATO ta aiwatar da ayar doka mai lamba hudu ta kundin yarjejeniyar kafa kungiyar wadda ta tanadi gudanar da taron gaggawa idan wani memba ya fuskantar barazana.

Karin bayani: Atisayen Rasha da Belarus ya tayar da hankali kasashen Yamma

Hakazalika jami'ar diflomasiyyar EU Kaja Kalas, ta tir da keta sararin samaniyar kasashen Tarayyar Turai a karo na uku, yayin da sakataren NATO Mark Rutte ya yaba da martanin gaggawa da dakarun kungiyar suka yi na kakkabo jiragen yakin na Rasha.

Sai dai a cikin wata sanarwa ma'aikatar tsaro ta Rasha ta yi watsi da wannan zargi da ke shirin bude sabon babin tankiya a tsakanin Moscow da kungiyar tsaro ta NATO.