1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta ba ´yan tawayen Libiya kunya

April 6, 2011

`Yan tawayen Libiya sun zargi NATO da nuna sako-sako ga dakarun shugaba Muhammar Ƙhaddafi

Hoto: AP

Dakarun ƙasar Libiya masu biyyaya ga shugaba Mohamar Ƙhadafi na cigaba da fafatawa da yan tawaye, wanda ke samun tallafi daga ƙungiyar tsaro ta NATO

Saidai yan tawayen sun koka game da yadda NATO ta ƙasa kawo ƙarshen gallazawa fararen hula da su ke zargin sojojin Khadafi da aikatawa.

Wani gungun ´yan tawaye ke salla, kusa da birnin Brega inda aka kwashe kwanaki da dama a na ɓarin wuta tskaninsu, da dakaru masu biyyaya ga shugaba Ƙhadafi.

A wata sanarwar da ya fido wannan Talata, babban hafsan hafsoshin ´yan tawayen, Janar Abdel Fattah Younes,ya zargi NATO da nuna sako-sako wajen yaƙar rundunar gwamnati bil haƙi da gaskiya,da kuma kasa taka rawar gani domin kare farar hula mussamman a birnin Misirata da ke kilomita 200 a gabacin Tripoli babban birnin Libiya.

Saidai shugabanin tawayen sun bayyana gamsuwa, game ga yadda jama´a ke amsa kiransu na shiga rundunonin yaƙi kamar yadda Sidyk ɗaya daga shugabanin ya bayyana:

"Da ƙarfin Allah matasan sun na amsa kira da himma, cemma dai haka su ke zaune, babu aikin fari ba na baƙi.Tun daga lokacin da mu ka buƙaci su shiga aikin sojan sakai, su ke tafe babu ƙaƙƙabatawa.

Da dama daga cikin su ba su taɓa riƙe bingida ba, amma da mun basu horo na sati guda ,shikenan sai su tafi filin daga."

A yayin da ta ke maida martani ga ƙorafin ´yan tawaye, mataimakiyar kakakin runduna NATO Carmen Romeno,ta tabbattar da cewa, za su yi iya ƙoƙarinsu, domin kare jama´ar birnin Misrata, wanda a cewarta fiye da kwanaki 40, suke ganin azaba daga dakarun gwamnatin Libiya.

Sai dai masu bin salsalar wannan yaƙi, sun yi hasashen cewar NATO za ta fuskanci raguwa, dalili da janyewar jiragen samar Amurika daga kai hare-hare ta sararin samaniya.

Har yanzu shugaba Ƙhaddafi na nuna turjiya ga hare-haren na NATO da ´yan tawaye.Ta fannin diplomatiya ya naɗa saban ministan harakokin waje Abdelati Obeidi, wanda zai gaji Moussa Koussa da yayi saranda kuma ya gudu zuwa Birtaniya.

Ita dai gwamnatin ƙasar Libiya, ta bakin kakakinta Musa Ibrahim, ta ce a shirye ta ke, ta hau tebrin shwara domin kawo ƙarshen rikicin:

"Shugaba Ƙhaddafi na matsayin mattatara ne na haɗa kan ƙabilu dabandaban na ƙasa, za mu iya girka gwamnatin haɗa ka a ƙarƙashin sa, wadda za ta ɓullo da inganttatar demokraɗiyar ta hanyar yaƙi da cin hanci da rashawa samar da ´yanci da walwala ga jama´a da kuma ´yancin faɗin albarkacin bakin ´yan jarida."

Suma ´ya´yan shugaba Muhamar Ƙhaddafi sun yi tayin warware rikicin ta hanyar sulhu matakin da ´yan tawaye su ka yi watsi da shi.

Faƙat a cewar su, hanya ɗaya tilo ta warware wannan rigima itace Ƙhaddafi ya sauka daga kujera mulki.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed Tijani Lawal