1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta fafata da Taliban a Kabul

September 14, 2011

Dakurun ƙawance a Afganistan sun gamu da farmakin 'yan Taliban mafi ɗaukar tsawon lokaci ana fafatawa, bayan Talban sun yi kutsen ba zata

Hayaƙi ke tashi a helkwatar NATO da ofishin jakadancin Amirka dake Kabul bayan harin 'yan TalibanHoto: dapd

A ƙasar Afganistan har izuwa safiyar yau laraba dakarun NATO sun ci gaba da kakkaɓe yan taliban da suka kai farmaki mafi girma a Kabul tun jiya da rana. Dakarun NATO na amfani da jiragen helikwapta a harin da suke kaiwa kan wani dogon gini dake tsakiyar wuraren da ake gani sunfi tsaro a ƙasar inda aka ɗauki sa'o'i 15 ana fafatawa. Wata majiya a Kabul ta shaidawa DW cewa an ci gaba da fada cikin dare, kuma da gari ya fara wayewa ma sai aka yi ta jin ƙarar facewar bama-bamai da ta shin bindigogi, a ci gaba da dakarun tsaro ke yi na kakkaɓe mayaƙan da suka yi musu shigar bazata kuma aka fara fafatawa tun a jiya. Dakarun Afganistan na bin daki-daki a dogon ginin, domin neman wadanda suka maƙale a ciki. Wannnan dai shine hari mafi daukan sa'o'i da aka yi ana fafatawa tun shekaru goma da Amirka ta jagoranci ƙawayenta a mamayar Afganistan, farmikin wanda bisa dukkan alamu an tsarashi ne, ya halllaka aƙalla mutane bakwai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu