1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO ta fara jigilar jiragen yaki F-16 zuwa Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
July 10, 2024

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne ya yi wannan shelar a taron NATO, inda ya bayyana cewar jiragen yakin za su yi shawagi a sararin samaniyar Ukraine a wannan bazarar don kare kanta daga farmakin Rasha.

Irin jiragen F-16 da kasashen NATO ke tura wa Ukraine
Irin jiragen F-16 da kasashen NATO ke tura wa UkraineHoto: Mindaugas Kulbis/AP Photo/picture alliance

Kasashen da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO sun fara mika jiragen yaki samfurin F-16 zuwa kasar Ukraine domin karfafa tsaron kasar da Rasha ta mamaye. Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi wannan shelar a taron NATO da ke gudanar a Washington na Amurka, inda ya bayyana cewar jirage za su yi shawagi a sararin samaniyar Ukraine a wannan bazarar don tabbatar da cewa ta ci gaba da kare kanta  daga farmakin Rasha.

Karin bayani: Ko Jamus za ta iya jagorancin NATO a Turai?

Sannan fadar mulki ta White House ta kara da cewa kasashen Beljiyam da Norway sun kuduri aniyar samar wa Ukraine da karin jiragen saman, wadanda Uraine ta fara nema jim kadan bayan harin da Rasha ta kai a  Fabrairun 2022, amma ba ta same su ba sakamakon rashin kwarewar sojojinta wajen jan jiragen F-16. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky da ke halartar taron NATO ya nuna cewar kasarsa na bukatar samun jiragen yaki 130 domin ta kama kafar Rasha, amma kasashen yamma sun yi alkawarin samar mata kasa da guda 100.