1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO ta gargadi Rasha kan keta sararin samaniyar mambobinta

September 23, 2025

A baya-bayan nan Rasha ta rika keta hazon wasu kasashen Turai mambobin NATO tana kai wa Ukraine hari.

Shugaban Kungiyar Tsaro ta NATO Mark Rutte
Shugaban Kungiyar Tsaro ta NATO Mark RutteHoto: Geert Vanden Wijngaert/REUTERS

Babban Sakatare Janar na Kungiyar Tsaro ta NATO Mark Rutte ya gargadi Rasha mai yaki da Ukraine da ta daina keta sararin samaniyar kasashe mambobinta tana kai wa Ukraine hari.

Rutte ya ce ayyukan da Rasha ta yi kwanan nan ciki har da bi da jirage a sararin samaniyar Poland da Romania da Estonia "rashin kwarewa ne a fili."

NATO sun dakile jiragen yagin Rasha a sararin samaniyar Estonia

NATO ta raka jiragen yakin Rasha suka fita daga sararin samaniyar Estonia a makon da ya gabata.

Ya kara da cewa kungiyar za ta ci gaba da tantance hadarin abinda Rasha ke yi sannan ta sanar da matsayarta.

Atisayen Rasha da Belarus ya tayar da hankali kasashen Yamma

Sau da dama kungiyar Tarayyar Turai EU ta sha gargadin Rasha kan bi ta sararin samaniyar 'ya'yanta tana kai wa Ukraine hari.