Amirka na fatan sasanta Rasha da Ukraine
January 10, 2022Talla
Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce yana fatan tattaunawar za ta samar da hanyar warware rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, amma ya gargadi Rasha ta kuka da kanta, idan ta sake kai wani hari kan Ukraine.
"Ina maraba da taron da zai gudana a yau, da kuma wanda za a yi a tsakiyar mako. Amma ba na tsammanin tarukan za su warware dukkan batutuwan. Abin da muke fata shi ne, mu amince a kan hanyar da za a bi, mu amince kan jerin tarurrukan da za a yi, mu amince kan tsari. Don haka bana ganin tarukan da aka tsara za su magance matsalolin."