1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta lalata tashar telebijan a Libiya

July 30, 2011

Ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ta ce ta yi luguden wuta akan gidan telebijan Libiya inda ta lalata kayan aikin watsa labarai

Jana'izar waɗanda suka rasu sakamakon hare-haren NATO a LibiyaHoto: picture-alliance/dpa

Rundunar ƙungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ba da sanarwa lalata wasu na'urorin yaɗa labarai guda ukku na tashar gidan telebijan Libiya bayan hare-hare ta jiragen sama da rundunar ta kai. A cikin wata sanarwa da ya bayyana kakakin rundunar, Kanal Roland Lavoie ya shaida cewa kai farmaki a ƙafar watsa labaran wani yunƙuri ne na karya lagon ɓaɓatun da shugaba Gaddafi ke yi sannan kuma ya ci-gaba da cewar:

" Jawaban da Gaddafi ke ci gaba da yi ta kafafen yaɗa labarai na bayyana manufarsa ta saka ƙiyaya a zukatun jama'ar ƙasar na cigba da zubar da jini don haka ya zama dole mu ɗauki mataki."

Gidan telebijan na Libya wanda ke ci gaba da watsa shirye-shiryensa ya bayyana wata sanarwa wacce a ciki ya ce mai'aikatansa ukku suka rasa rayukansu yayin da wasu 15 suka jikata. Kuma shugaban gidan telebijan ɗin ya yi Allah wadai da harin da ya kira na ta'addanci.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas