1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceEstoniya

NATO ta tabbatar da harbo jirgin Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
May 19, 2026

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta tabbatar da cewa daya daga cikin jiragenta na yaki samfurin F16 da ke aikin bayar da kariya a wani sansani da ke Lithuania ya harbo wani jirgi mara matuki a sararin samaniyar Estonia.

Jirgin Ukraine mara matuki ya fuskanci hari bisa kuskure
Jirgin Ukraine mara matuki ya fuskanci hari bisa kuskureHoto: Genya Savilov/AFP

Estonia da Latvia dukkaninsu sun ankarar da barazana na kutsen jirgi mara matuki a sararin samaniyar su. Babu tabbacin ko suna nufin abu daya ne ko kuma jirage mabanbanta.

Sojojin Estonia sun ce wani jirgi mara matuki ya shiga sararin samaniyar kasar da misalin karfe tara agogon GMT a yau Talata, daga bangaren Rasha inda ya yi kutse zuwa kudu maso gabashin kasar kuma nan take jirgin yakin NATO na Romania da ke shawagin atisaye ya harbo jirgin da misalin karfe 12: 14 agogon kasar.

NATO ta ce ana gudanar da bincike kan lamarin.