NATO ta yaba wa yunkurin Trump na sulhu a Ukraine
November 27, 2025
Talla
Mark Rutte ya ce an sa himma sosai wajen kokarin yin sulhu a yakin Rasha da Ukraine a saboda haka ina gode wa shugaba Trump kamar yadda ya shaida wa yan Jarida a ziyararsa zuwa Iceland.
Shawarar tsagaita wutar ta sami tagomashi yayin da tattaunawa ta kankama tsakanin Jami'an Rasha da Ukraine da Washington da kuma na tarayyar Turai inda aka yi tattaunawa a Geneva da kuma Abu Dhabi.
Amurka dai ba ta wallafa sabon jadawalin shawarwarin ba, sai dai Trump ya ce an yi masa kwaskwarima daga shawarwari 28 da ya zayyana tun da farko wanda Kiev da aminanta na Turai suka ce sun karkata ga Kremlin.