NATO: Trump ya bukaci Jamus ta kara tallafi
April 3, 2019Shugaban Amirka Donald Trump ya jinjinawa kasashe mambobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO dangane da kara gudunmawar kudi na tafiyar ayyukan rundunar tsaron ta yammacin Turai. Sai dai duk da haka ya bukaci kasashen su rubanya tallafi yana mai cewa har yanzu Amirka ce ke daukar nauyi mai yawa na tafiyar da kungiyar. Musamman Trump ya soki lamirin Jamus saboda kin kara gudumawar kudi ga kungiyar.
A ranar Talata shugaban ya gana da sakataren kungiyar tsaron ta NATO Jens Stoltenberg a Washington inda ake shirin gudanar da bikin cikar kungiyar NATO shekaru 70 da kafuwa. Shugabannin biyu sun yi musayar kalamai masu dadi da raha sabanin baya inda Trump ya baiyana kungiyar ta NATO da cewa ta zama tsohuwar yanayi inda ya yi barazanar duba yiwuwar tsame Amirka daga cikin kungiyar idan kasashe basu rubanya tallafinsu ba.