NATO za ta fadada aikin ba da horo a kasar Iraki
February 12, 2020Babban sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce a shirye kungiyar take ta fadada aikin ba da horo a kasar Iraki.
A lokacin da yake magana yayin wani taron ministocin tsaron kasashen kungiyar NATO a birnin Brussels, Stoltenberg ya ce yana sa rai ministocin za su amince da matakan ba wa Irakin karin tallafi a yakin da take yi da ta'addanci.
Ya ce: "NATO na da sansanin ba da horo a Iraki, muna kuma kasar ne bisa gayatar wgamnatin Iraki, za kuma mu ci gaba da zama a kasar matsawar gwamnatin Iraki na maraba da zamanmu a can."
Majiyoyi daga NATO na cewa aikin ba da horo na kawancen kasa da kasa don yaki da 'yan ta'addar kungiyar IS, ka iya zama wani bangare na aikin kungiyar kawancen, amma bisa sharadin samun amincewar gwamnatin Iraki, kamar yadda Stoltenberg ya kara jaddadawa.