Naurar leken asirin koriya ta Arewa ta gamu da cikas
May 31, 2023Talla
Koriya ta Arewa ba ta da tauraron dan Adam ko daya a sararin samaniya. Sai dai Shugaba Kim Jong Un ya jima da mayar da samar da tauraron dan adam na leken asirin soja a matsayin babban ginshiki na gwamnatinsa, a lokacin da sojojin Amirka da na Koriya ta Kudu ke ci gaba da atisayen hadin gwiwa.
Koriya da Kudu da Japan da Amirka sun yi Allah wadai da wannan gwajin wanda suka ce ya saba wadokokin Majalisar Dinkin Duniya da ya haramta wa Pyongyang gwajin makamai masu linzami.
Koriya ta Arewa ta sha alwashin sake gyara tauraron tare da neman nasarar harba shi a sararin samaniya nan bada jimawa ba bayan ta amince cewa na'urar na cike da kura-kurai.