1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta karyata likitocin Jamus a kan Navalny

Abdul-raheem Hassan AH
August 25, 2020

Fadar gwamnatin Rasha ta karyata zargin likitocin Jamus wadanda suka gano cewar guba ce aka bai wa jagoran 'yan adawar kasar Rasha Alexei Navalny.

Russland Alexej Nawalny
Hoto: Getty Images/AFP/K. Kudryavtsev

Yanzu haka dai dan gwagwarmayar na Rasha Alexei Navalny, na yunkurin farfadowa a gadon jinya a Jamus, bayan da binciken likitoci ya nuna cewar an yi yunkurin ba shi guba don hallaka shi. Yanzu haka dai gwamnatin Jamus na kokarin ganin ceto ran Navalny shi ne abin da ke kan gaba, kamar yadda Steffen Seibert kakakin shugabar gwamnati Angela Merkel ya nunar: ''Abu na farko dai shi ne a jira sakamakon binciken likitoci da zai fito. Likitoci da ke kula da Navalny da iyalansa ne kadai za su iya samar da bayanai kan halin da Navalny yake ciki a yanzu haka da kuma abin da ke faruwa.“

Jamus ta jaddada binciken da likitocinta suka gudanar a kan Navalny

Angela Merkel Shugabar gwamnatin JamusHoto: Getty Images/AFP/C. Simon

Alexei Navalny mai shekaru 44, lauya ne mai fafutukar yaki da rashawa a Rasha, ya zama jigo ga 'yan adawar kasar da ke shiga kafar wandon siyasa guda da Shugaba Vladimir Putin. Gidan jarum ya zama ba sabon wurin shigar Navalny ne ba, sakamakon shirya zanga-zangar adawa da gwamnati abin da shugaban Rasha bai yarda da shi ba, hakan ne ma ya sa ake karfafa zaton cewar da hannun gwamnatin Rasha a wannan al'amari na guba da aka bai wa jagoran 'yan adawar na Rasha. 

Sannan shi kansa kokarin saka jinkiri wajen kai Navalny Jamus daga Rashar don yi masa jinya, ya sa ana zato da walakin. Sakamakon bincike na asibitin Jamus da ke karbar jinyan Navalny ya ta’allaka ne kan bincike mai zurfi, a cewar wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas da shugabar gwamnati Angela Merkel: “Bukatunmu suna nan daram, tun da dai akwai zargi mai karfi, musamman kan sa masa gubar, wannan dole ne a gudanar da binciken kirki. Amma a matakin da ake yanzu, muna so mu saurara mu ga matakin da zai fito daga bangaren likitoci.”


Rasha ta karyata zargin likitocin Jamus cewa guba aka ba Navalny 
Duk da cewa zargin gwamnati da hannu a yunkurin kisa ko nakasa madugun adawar na kara karfi kan gwamnatin Shugaba Vladmir Putin, amma tuni fadar gwamnatin Kremlin ta karyata zargin tare da fatali da duk wani bincike da suka kira na gaggawa.

Vladimir Putin Shugaban Kasar RashaHoto: Reuters/A. Druzhinin

A  shekarar ta 2010 tauraron Navalny ya fara haskawa a Rasha, lokacin da ya fara bankado ayyukan rashawa a shafukan yanar gizo. Sannan a hankali binciken rashawa na Navalny ya fara karkata kan Shugaba Putin da gwamnatinsa.

Navalny ya jagoranci zanga-zanga da dama na Allah wadai da gwamnatin Putin a 2011 zuwa 2013. Ya zama shugaban sabuwar jam’iyyar adawa a 2013 ya kuma zo na biyu a takarar zaben da ya kira magudi ya hana shi zama na farko.