1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nawalnaya ta sami lambar yabo ta DW

Abdoulaye Mamane Amadou
June 8, 2024

Tashar DW ta ba wa mai dakin madugun 'yan adawar Rasha Alexe Navalny wato Julia Nawalnaya da kyautar gwarzuwar fadar albarkacin baki ta 2023

Yulia Navalnya im Interview mit der DW
Hoto: DW

 A yayin bikin karbar kyautar a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, Julia Navalnaya ta bayyana cewa 'yancin fadar albarkacin baki wani babban makami ne mai matukar muhimmanci kuma duk da kisan mijinta da Shugaba Putin ya yi, har yanzu akidunsa da manufofinsa suna raye kuma abin koyi ga jama'a.

Gidauniyar FBK mai yaki da cin hanci da Rashawa da  Alexeï Navalny ya assasa a kasar Rasha shekaru 13 da suka gabata ta samu kai wannan matakin ne bayan da mai dakin marigayin Navalny, Julia Nawalnaya ta ci gaba da jajircewa tare da dorawa inda mai gidanta ya tsaya a fannin yaki da cin hanci da tabbatar da dimukuradiyya da walwala, wannan kuwa duk da kisan gillar da aka yi wa mijinta a cikin watan Fabrairu.

Karin Bayani:Kyautar DW ta 2024 ta 'yancin fadar albarkacin baki

Lambar yabo ta DW ta 'yancin fadin albakacin bakiHoto: Ronka Oberhammer/DW

A kasaitaccen bikin da DW ta shirya na ba ta labar yabon, Navalnaya ta ce Shugaba Putin ya rabata da abin kaunarta, ya raba ta rabin ranta amma kuma wannan wata dama ce a gareta ta kara jaddada manufofinsa.

A tsawon shekarun da ta yi tana jagorantar gidauniyar, Navalnaya ta yi namijin kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa a Rasha, kana gidauniyar ta fallasa duk wasu dabi'u da gwamnatin Rasha ke yi na cin han ci in ji babban daraktan DW Peter Limbourg a yayin da yake mika kyautar ga Navalnaja a birnin Berlin.

Gidauniyar da ke yaki da cin hanci da Yulia Navalnaya a Rasha sun saka haske kan duhun daren cin hanci da gurbatacciyar gwamnatin Rasha ke aikatawa. Ukraine na fama da mamayar Rasha da alama mutane da dama na yarda da farfagandin da gwamnatin Moscow, hakan kuma wasu miliyoyin 'yan kasar ba sa nuna amincewa, wadannan jama'ar na da bukatar kafafaen yada labarai na hakika masu muhimman labarai na zahiri da irin su DW ke bayarwa, ana samun sahihan labarai da manufofi na gari ta hanyoyin intanet da tauraron dan Adam."

Karin Bayani: Mai dakin jagoran adawar Rasha ta roki EU a kan Rasha

Yulia Navalnaya a Berlin 2024Hoto: Ebrahim Noroozi/AP/picture alliance

Misis Navalnaya dai ta bayyan cewa 'yancin fadar albarkacin baki wani muhimmin makami ne da mijinta da gidauniyarsa suka rike don tunkarar Putin a tsawon shekaru 13 a yayin da take karbar kyaurat ta DW, kana daga nan ne kuma gwarzuwar 'yancin fadar albarkacin baki ta bana ta bayyan cewa za ta ci gaba da tafiyar da manufofin mijinta.

Navalnaya ta ce yana da muhimmanci na sanar da abokan aikina na wannan gidauniyar da Navalny ya kafa shekaru 13 da suka gabata da wannan abin farin ciki, a duk tsawon wadannan shekarun 13 shekaru Shugaba Putin ya ragargaza tsarin zabe ya hana zanga zanga ta hanyar muzgunawa 'yan jarida mumsaman ma wadanda ba sa fadar abinda yake son ji, to amma kuma duk da haka ya kasa nasara, gaskiya ne ya kashe mijina, to amma kuma bai kawar da burbushin manufofinsa ba.

Karin Bayani: Navalnaya: Duniya na bukatar tashi tsaye a kan Putin

Shi kuwa ministan kudin Jamus Christian Lindner guda daga cikikin manyan baki a babban taron na ba wa Navalnaya kyautar gwarzuwar 'yancin fadar albarkacin bakin ta bana cewa ya yi .

Ministan kudin Jamus Christian Lindner wajen bayar da lambar yabo ga NavalnayaHoto: Ronka Oberhammer/DW

Christian Lindner,  ya ce a yau DW kun bayar da wannan muhimmiyar kyauta ta 'yancin albarkacin baki, zan iya cewa kyauta ce da ke mutunta 'yanci da tunanin kowane mahaluki a doron kasa kana kyautar na kara tunatarwa kan alfanun dimkuradiyya da hakin dan Adam.

Daukacin wadanda suka gabatar da jawabai a yayin bikin sun jaddada goyoyn bayansu ga batun 'yanci da fadar albarcin baki, baya ga jinjina wa kusoshin gidauniyar ta FBK kama daga Navalny har i zuwa ga shakikinsa kuma lauya mai zaman kansa a Rasha Ivan Zhdanov.

Alexeï Navalny dai ya kafa gidauniyar ce mai suna FBK a shekarar 2011 da manufar tona asirin karbar na goro da aikata cin hanci da jami'an gwamnati ke yi a kasar Rasha, sai dai daga bisani ya rikide ya koma wani cikakken abokin hamayyar Shugaba Putin.