Nawaz Sharif ya zama firaministan Pakistan
June 5, 2013Majalaisar dokokin Pakistan ta zabi dan siyasan nan da ke da ra'ayin rikau wato Nawaz Sharif a matsayin sabon firaministan kasar. 'Yan majalisu 244 daga cikin 342 ne suka kada kuri'ar yin na'am, da shugaban jam'iyar PML-N da ta zo ta daya a zaben watan mayu a matsayin sabon jagoran Pakistan.
A cikin jawabin da ya yi, Sahrif ya yi kira da a kawo karshen takaddama da ake yi a kan hare-haren jiragen Amirka da ke sarrafa kansu da kansu a yankin kan kiyaka da Afhganistan. Hakazalika ya yi alkawarin sa kafar wando guda da cin hanci da rashawa da kuma 'yan taliban. Sharif har wa yau ya ce zai dauki matakan da suka wajaba domin magance matsalar makashi da kuma na tatalin arzikin da kasarsa ke fama da su.
Tuni dai ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya aika wa Nawaz sharif da sakon taya murna, inda ya ce zaben da a ka yi cikin 'yanci da walwala wani mataki ne na inganta demokaradiyar kasar Pakistan. Shi dai Nawaz Sharif mai shekaru 63 da haihuwa, ya taba rike mukamin firaminista so biyu a rayuwasu a shekarun 1990.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu